Tuesday, 14 January 2020

Mutumin da DSS ta kama yana amfani da layin diyar shugaban kasa, Ya kai kara kotu inda yake bukatar a biyashi diyyar Miliyan 500

Mutuminnan da hukumar 'yansandan farin kaya ta DSS ta kama saboda amfani da tsohon layin diyar shugaban kasa, Hanan Buhari aka kuma tsareshi tsawon makonni 10 duk da cewa shi yayi ikirarin cewa sayen layin yayi, Anthony Okolie ya kai kara kotu.
Okolie ya kai karar Hanan Buhari da hukumar DSS da kuma kamfanin MTN inda yace su biyashi Naira Miliyan 500 saboda cin zarafinshi da aka yi.

Shi dai ya sayi layinne bayan da Hanan Buhari ta dade bata yi amfani dashi ba kuma kamfanin MTN ya sake mayar dashi sabon layi ya sayar masa, yace har rasidin da ya sayi layin yana nan kuma sai da ya nunawa DSS shi.

Yace an ajiyeshi a kulle inda aka jira Hanan Uhati dake kasar waje tana karatu tazo ta sa a sakeshi. Dan haka yanzu sai an biyashi diyya.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment