Pages

Sunday 26 January 2020

Na fuskanci matsala har da abokan aikina>>Dansandan da bai taba karbar cin hanci ba

Jami'in dan sanda, Francis Erahbor kenan da bai taba karbar rashawa ba a shekaru 29 da yayi yana aikin dan Sanda. A yanzu shine DPO na Itam, Karamar Hukumar Utu dake jihar Akwa Ibom.




A kwanannanne aka baiwa jami'in dansandan Kyautar karramawa ta Rikon Gaskiya da Amana a babban birnin tarayya Abuja bayan da yaki karbar rashawar Miliyan 6 dan ya bari a yi satar Mai a jihar Edo.

Yace a watan Aprilu na shekarar 1990 ya fara aikin dansanda kuma tun daga lokacinne ya  daukarwa kanshi alkawarin cewa ba zai karbi cin hanci ba.

Yace bayan da suka fito daga horaswa aka kaishi inda zai fara aiki sai yaga abinda aka gaya musu a ajan horaswar na yanda ake gudanar da ofishin 'yansanda ya banbanta da abinda ya gani na zahiri.

Yace Dubu 28 zuwa 29 ake bayarwa duk karshen watanni 3 dan gudanar da ayyukan ofishin 'yansandan saidai yace da taimakon jama'a yayi kokarin ganin Ofishin da yake yana tafiya daidai.

Yace ya fuskanci matsala har a wajan abokan aikinshi ta yanda wani lokacin idan aka kaishi waje sai kaga wasu jami'an 'yansandan na bukatar a musu canjen wajen aiki dan sun san cewa shi baya karbar cin hanci.

Saidai ya bayyana cewa matarshi ta bashi hadin kai inda tace koda gari zasu rika ci ta yadda su zauna ba tare da ya karbi cin hanci ba.





Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment