Monday, 13 January 2020

Na kasa samun sanatoci masu kadarar Biliyan 1 da zasu tsayamin a bada belina>>Abdulrashid Maina

Tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Abdulrasheed Maina ya toki kotu data saukaka mai sharuddan data saka na bada belinshi inda yace ya cika duk wani sharadi amma ya kasa samun sanatoci masu kadarar data kai Biliyan 1 da zasu tsaya masa a bada belin nashi.Maina wanda tun a watan Octoban shekarar data gabata yake tsare ya bayyana cewa ya samo sanatoci 2 da zasu tsaya masa amma basu da kadarar data kai ta Naira Biliyan 1.

Alkalin kotun dai ya bukaci Maina ya samar da sanatoci 2 wanda kowannensu yana da kadarar data kai Naira Miliyan 500 a Asokoro ko Maitama a babban birnin tarayya, Abuja sannan kuma dole Sanatocin su rika zuwa tare da maina zaman sauraren karatshi har a gama hakanan dole su bayar da fasfonsu har sai an kammala shari'ar.

Da yake mika kokensa a yau Litinin 13 ga watan Janairu, Maina ya bayyana cewa, a saukaka masa da wannan sharuda.

Saidai babbar kotun gwamnatin tarayyar dake Abuja tace akwai dalilin da yasa ta saka wadannan sharudda akan belin na Maina.

Ana zargin Maina da sama da fadi da Naira Biliyan 2.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment