Tuesday, 28 January 2020

Nidai idan matata ta kasheni dan Allah kada a kasheta, a barta ta kulamin da 'ya'yana

Bayan da babbar kotun gwamnatin tarayya ta yankewa Maryam Sanda data samu da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello hukuncin kisa ta hanyar Rataya, mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu akai.
Shidai wani likita me suna Dr. Usha Anenga ya bayyana cewa shi  yasan matarshi ba zata kasheshi ba amma idan bisa kaddara hakan ta faru to shi dai be yadda a kashe ta ba. A barta ta kula mai da 'ya'yanshi.

Ya kara da cewa yana so a jiye wannan magana tashi da yayi a dandalin Twitter a matsayin hujja a Kotu.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment