Tuesday, 14 January 2020

Niger: Buhari ya jajanta wa shugaba Issoufou kan kisan sojoji

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi wa Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou jaje ta wayar tarho bisa harin da masu tayar da kayar baya suka kai a Chinagodrar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar gwamman sojojin Nijar.


A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Garba Shehu ya fitar, Shugaba Buhari ya ce yana mika ta'aziyyarsa ga iyalai da abokan aikin wadanda suka mutu.

An kai harin ne ranar 9 ga watan Janairun 2020, inda aka kashe sojan kasar ta Nijar kusan 89.

Buhari ya yi Alla-wadai da harin, sannan ya jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da Nijar da sauran kawayenta domin kawo karshen ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.Faransa ita ma ta rasa sojojinta 13 sakamakon wani harin jirgi mai saukar ungulu a kasar Mali cikin watan Nuwamba.

Wani hari da aka kai a watan Disamba a Nijar ya zaburar da shugabannin yankin Sahel wajen yin kira ga kasashen duniya da su ba su tallafi a yakin da suke yi da masu ikirarin jihadi.

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment