Tuesday, 14 January 2020

Sai Litinin za a yanke hukunci kan zaben Abba da Ganduje- Kotun Koli

Kotun Kolin Najeriya ta ce sai ranar Litinin 20 ga watan Janairun 2020 za ta yanke hukunci kan shari'ar Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar PDP inda yake kalubalantar Abdullahi Umar Ganduje na jam'iyyar APC da kuma hukumar INEC.


Lauyoyin bangarorin sun shafe sama da awa daya suna tafka muhawara kafin alkalan suka yanke wannan hukunci.

A halin yanzu alkalan sun tafi hutu na dan lokaci inda ake sa ran dawowarsu na da dan lokaci kadan domin ci gaba da shari'a kan zaben jihohin Sokoto da Bauchi da Filato da Benue da kuma Imo.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment