Tuesday, 14 January 2020

Tafkin Chadi: An Kashe Wani Babban Kwamandan Kungiyar ISWAP

A wata sanarwa da kakakin rundunar kasashen yankin tafkin Chadi, Kanar Timothy Antigha ya sanya wa hannu, ta ce dakarun sun kashe mutum na uku mafi girma a kungiyar Amir Khalifa Umar.


Hakan ya faru ne bayan wani mummunan farmaki ta sama da dakarun suka kai, a wani yanki da ake kira Tumbin Sabon.

Shi dai Khalifa Umar na daga cikin manyan kwamandojin masu tasiri sosai a kungiyar dake ikirarin jihadi, da kuma ake nema ruwa a jallo, a cewar sanarwar.

Haka kuma Khalifa Umar ya kasance shine Alkalin Alkalan kungiyar ISWAP.

Da yake karin bayani kakakin hedikwatar rundunar sojojin saman Najeriya, Ibikunle Daramola, ya ce an sake kaddamar da munanan farmakin nan mai take ‘Operation Rattle Snake’ kan kungiyar Boko Haram da IS a yankin tafkin Chadi. A 'yan kwanakin nan dai, jiragen yakin Najeriya sun yi ta ruwan wuta a zirin yankin tafkin Chadi.

Rundunar sajojin saman Najeriya ta ce an sami nasarori sosai akan sansanoni da wuraren taraku da na ajiye makamai duk an ruguza su.

A baya-bayan nan dai rundunar hadin gwiwa ta tafkin Chadi dai na ci gaba da samun nasara tun bayan da aka nada sabon kwamanda, Majo Janar Ibrahim Manu Yusuf.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment