Sunday, 26 January 2020

Tauraruwar fim din India ta kashe kanta

Tauraruwar fina-finan India, Sejal Sharma 'yar shekaru 22 ta kashe kanta a dakinta dake birnin Mumbai na kasar a Ranar Juma'ar data gabata.Matashiyar jarumar ta shaharane wajan yin Dirama irin wadda ake nunawa a gidajen talabijin inda Diramar data fi fito da ita sosai aka santa itace ta Dil Toh Happy Hai Ji wadda gidan talabijin na Star Plus ke nunawa.

Kafar watsa labarai ta Times of India ta tabbatar da mutuwar jarumar. Ta kuma yi aiki da mayan Jaruman India irinsu Aamir Khan.

A shekarar 2017 ne ta Je Mumbai dan fara shirin fim inda ta bayyana cewa ta sha fama da mahaifanta kamin su yadda ta fara yin fim.

Diramarta ta Dil Toh Happy Hai Ji ta karbu a India sosai inda har ta bayyana cewa butinta ya cika na zama tauraruwar jaruma.

Badai a bayyana dalilin kashekannata da ta yi ba.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment