Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya koka kan yanda jami'o'in kasarnan ke samar da dalibai wanda basa iya taimakawa wajan ci gaban tattalin arzikin Najeriya.
Ya bayar da misalin cewa dalibine ya karanci inijiya amma na'urar sanyaya dakinshi ta lalace ba zai iya gyarata da kanshi ba saidai yaje Sabon Gari wajan makaniken da baijr makaranta ba ya mai gyaran.
Yace hakanan dalibi ya kammala karatu ya samu gwalin Digirinsa, idan akan bashi fili aka basahi Jari be san ta inda zai fara ba.
Yace dolene jami'o'i su saka tsari wanda zai rika baiwa dalivan da suke karantarwa itin ilimin ci gaban da al'umma ke bukata.
Yace daya daga cikin abinda ya dade yana magana akai shine wai me yasa ake amfani da turanci a matsayin yaren koyar da karatun Boko? Me yasa mutum zai iya karatu da yaren China ko na Jamusanci ko Faransanci kuma ya zama Likita?
HRH Muhammad Sanusi II CON, Sarkin Kano presenting his speech at Federal University of Gusau.— Kano Emirate Council (@masarautarkano) January 25, 2020
Allah ya taimaki Sarki. pic.twitter.com/ZcGAWKLYmj
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole
No comments:
Post a Comment