Tuesday, 14 January 2020

Yan Bindgia Sun Kashe Mutane 35 A Kaduna, Sun Kuma Bukaci A Ba Su Naira Milyan Dari A Matsayin Kudin Fansar Mutane 58

Kimanin mutane 35 suka rasa rayukansu kuma an yi awon gaba da 58 sakamakon harin bazatan da yan bindiga suka kai garuruwa 10 a karamar hukumar Chikun da Birnin Gwari na jihar Kaduna.


Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hare-hare kauyukan ne ranar 6 ga watan Junairu inda suka bukaci kudin fansa milyan dari daga hannun iyalan mutane 58 da suka sace.

Hare-haren ya tilastawa mutane arcewa daga muhallansu inda suka koma kwana a cikin makarantun gwamnati.

Shugaban kungiyar al'ummar kudancin Kaduna, Jonathan Asake, ya ziyarci wadanda hare-haren ya shafa ranar Litinin inda ya gana da wani fasto, Habila Sarkin Noma, don jajen ibtila'in da ya afka musu.

Ya ce "yan bindigan sun lashi takobin cewa sai mun biya kudin fansan N100m idan muna son ganin yan uwanmu da rai."

Yayi zargin cewa "makiyaya ne suka kawo harin saboda sun saba zuwa lalata gonakinmu kuma suyi barazanar kashemu idan muka ce uffin."

"Wasu lokutan idan suka kawo hari kuma sukayi awon gaba da mutane, muka biya kudin fansa amma duk da haka su kashesu."

"Amma harin da ya auku ranar 6 ga Junairu, 2020 ne mafi tsanani, sun kashe mutane 35 kuma sunyi garkuwa da mutane 58 a kauyuka 10.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment