Tuesday, 14 January 2020

Yanda dan sanda yawa wata mata tsirara

Wata mata me suna Mercy Okoro 'yar shekaru 28 ta zargi DPOn dan sanda, Asanayin Ibok a Ekpan, karamar hukumar Uvwie dake jihar Delta da yi mata tsirara haihuwar uwarta.
Lamarin ya farune a tanar 10 ga watan Janairu da misalin karfe 3 na yamma kamar yanda Mercy ta bayyanawa manema labarai. Tace 'yansandan sun kuma kama mahaifiyarta,Lucy.

Duk wannan ya farune sanadiyyar rashin jituwar da aka samu tsakaninsu da wani mutum dake haya a gidansu kuma sun bashi lokaci ya tashi saboda baya biyan kudin haya amma yaki yadda ya tashi.

Daga baya yaje ya kira musu 'yansansa shine Mercy tace, dansandan ya tattakata ya kuma kwance mata zane inda ya kamata ita da mahaifiyarta ya sakasu cikin motar 'yansanda zuwa caji Ofis.

Tace sai bayan zuwansu Caji Ofisne ta gane cewa ashe DPO ne acan ma tace ta sha mari wan kuma har saida ta suma inda tace daga baya wata 'yarsanda ta gwagwada mata Barkonon tsohuwa a Ido.

Mahaifiyar Mercy, Lucy ta tabbatar da wannan zargi inda tace suna neman gwamnati da kungiyoyin kare hakkin bil'adama su shigo lamarin.

Saidai da Punch ta tuntubi DPOn da ake zargi, ya karyata inda yace shi bama ya nan a lokacin da lamarin ya faru.

Shima dai kwamishinan 'yansadan jihar,Hafiz Inuwa ya bayyana cewa, ba gaskiya bane labarin da Mercy ta bayar dan DPOn da take zargi baya nan a lokacin da lamarin ya faru tsakaninta da me haya a gidanta.

Saidai shugaban kungiyar kare hakkin bil'adama ta HRBO dake jihar, Omon-Irabor ya bayyana cewa, da gaske 'yansandan sun ci zarafin matar inda yace saida suka bayyana mai cewa sun daukeshi hoto sannan ya tsaya suka tattauna.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment