Thursday, 16 January 2020

Zamu tabbatar da ganin mata sun samu ilimi kuma an daina auren wuri>>Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bude sabuwar hedikwatar ma'aikatar mata ta kasa a babban birnin tarayya, Abuja, Yau Alhamis. Shugaban ya bayyana cewa suna kokarin ganin an kawar da auren wuri da kuma baiwa mata ilimi.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, ilimantar da iyaye mata yanzu da wanda nan gaba zasu zama iyaye suma abune me matukar muhimmanci da kuma ya kamata ace kowa ya saka hannu an yi dashi.

Yace sun baiwa wannan batu muhimmanci a gwamnatinshi dan ganin mayar da matan da suka kasa samun ilimi ko kuma suka fara suka bari saboda wasu dalilai na al-ada ko tattalin Arziki, kamar yanda me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya bayyanar.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment