Pages

Friday 14 February 2020

Bazan Yanke Hulda da harkar fim ba koda na yi Aure>>Tauraruwar Kannywood

SAPNA Aliyu Maru ta bada tabbacin cewa ba za ta yanke hulɗa da harkar fim ba ko da ta yi aure.

Ta ce za ta rinƙa ɗaukar nauyin shirya finafinai bayan ta yi aure.


Fitacciyar jarumar ta waɗannan bayanai ne a daidai lokacin da wasu cewa ta bar Kannywood, ta rungumi harkar kasuwancin ta.

Sapna, wadda daga tauraruwar ta ta rinƙa haskawa a shekaru biyu zuwa uku da su ka gabata, ta ce har yanzu ita cikakkiyar jaruma ce a masana'antar finafinai ta Kannywood.

A lokacin da ta ke tattaunawa da mujallar Fim, Sapna ta yi bayyana matsayin ta da cewa, "Ni abin da zan faɗa, Sapna dai ba ta daina yin fim ba, domin fim sana'a ta ne, babu yadda za a yi na daina yi sai dai idan na yi aure, kuma ko da na yi aure zan ci gaba da yin furodusin kamar yadda na ke yi.

"Illa iyaka dai a yanzu akwai wasu abubuwa da na ke yi da su ka shafi harkar kasuwanci wanda a yanzu su na sa a gaba. 

"Kuma ko da aka daina gani na, ina yin furodusin, ba na fitowa ne dai a ciki, don haka ake ganin kamar na daina yi, domin ko rajistar da aka yi a Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano na je na yi a matsayi na na furodusa, don haka ka ga ai ni cikakkiyar 'yar fim ce."

Jarumar ta ci gaba da cewa, "Kamar yadda na faɗa maka, ina harkar kasuwanci, don haka na kan je na saro kaya na raba ko na zuba a kanti na, don haka sai ya zama babu lokaci a gare ni da zan gudanar da harkar da har zan samu lokacin da wani zai gayyace ni fim ɗin sa, don haka idan na ce zan karɓi aikin mutane, ban san yadda zan yi da su ba."

Fim ɗin Sapna na ƙarshe shi ne 'Wata Rana', wanda ita ce ta shirya shi. 

"Ni ce jarumar fim ɗin wanda mu ka yi da Adam A. Zango," inji ta. "Ina ganin ya kai kamar shekara uku yanzu. To tun daga shi sai dai na yi furodusin idan na samu lokaci."

Ko yaya Sapna ta ke kallon harkar fim a yanzu? Sai ta ce, "To wani lokacin dai zan iya cewa daga nesa na ke kallon ta, domin yanzu ba ko yaushe na ke samun lokacin shiga cikin harkar ba. Amma duk da haka, idan na shiga ina ganin ci-gaban ta, domin na kan ga sababbin abubuwa na cigaba. 

"Don haka zan iya cewa harka fim ta na samun cigaba, kuma ina fatan cigaban ya rinƙa samuwa nan gaba."

Daga ƙarshe, jarumar ta yi fatan samun haɗin kan 'yan fim domin a samu cigaba da zaman lafiya mai ɗorewa a cikin masana'antar.







Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment