Friday, 7 February 2020

Yaro dan shekara 10 yawa yarinya 'yar shekaru 13 ciki

Wata yarinya 'yar shekaru  13 da haihuwa 'yar Kasar Rasha me suna Dasha Sudnishnikova dake dauke da juna Biyu ta bayyana cewa saurayinta dan shekaru 10 ne ya mata cikin.Saidai maimakon abin ya daga mata hankali, yarinyar ta rika son neman samun daukar nauyi daga manya-manyan kamfanoni inda takan saka bidiyo da hotunanta a shafukanta na sada zumuta. Takan yiwa kanta taken cewa 'yar shekaru 13 da ciki.

Kuma hakan ya jawo mata mabiya sosai inda ta dauki hankulan ma'abota shafukan sada zumuntar.

Mahaifiyar yarinyar, Elena ta bayyana cewa, da farko sun sha wani abune ta ci ya kumbura mata ciki amma daga baya da suka fara ganin alamun juna biyu sai suka je aka yi gwaji kuma aka tabbatar diyar tasu na da ciki.

Tace ba zata zubarwa da diyartata cikin ba dan watakila shi kadaine rabonta.

Ta kuma sha alwashin baiwa diyartata duk gudummuwar da take bukata duk da yake cewa itama tana fama da cutar Kansa, kamar yanda Mirror ta ruwaito.
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

No comments:

Post a Comment