fbpx
Monday, September 27
Shadow

2023: Babu fa wanda zai takura mana mu zabi dan kudu>>Dattawan Arewa

Kakakin kungiyar dattawan Arewa ta, NEF Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, babu wamda zai takurawa ‘yan Arewa su zabi dan kudu a matsayin shugaban kasa a 2023.

 

Yace masu neman dole-dole sai dan kudu ya zama shugaban kasa a 2023 ragwayene.

 

Yace su tashi tsaye su nemi kuri’ar ‘yan Arewa ba wai kawai su ce dole sai an zabesu ba. Yace duk wanda zai zama shugaban kasa daga kudu sai ya tabbatar musu da cewa ba kudu kadai zaiwa aiki ba.

 

Yace basu son shugaban da zai zo ya rika nuna banbanci. Ya bayyana hakane a hirar da The Nation ta yi dashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *