fbpx
Thursday, July 29
Shadow

2023: Baku isa ku sa mu zabi wanda bamu so ba>>Dattawan Arewa ga Gwamnoni Kudu

Kungiyar Dattawan Arewa ACF, ta shawarci gwamnonin kudancin Najeriya da su bi tafarkin da ake bi wajen zaben shugabanni daga wurin masu kaɗa ƙuri’a, ba kawai suna zaune a kai musu mulki ba.

Kungiyar ta yi wannan magana ce a matsayin martani kan matsayar da gwamnonin kudancin Najeriyar suka cimma a ranar Litinin, cewa suna son shugaban ƙasar da za a zaɓa a 2023 ya fito daga yankin kudun.

A wata hira da BBC Hausa, kakakin kungiyar Dattawan Arewan Dr Hakeem Baba Ahmed, ya shaida wa BBC cewa kalaman gwamnonin kudun barazana ce kawai wadda ba za ta bai wa ‘yan arewa tsoro ba.

Ya ce “Mu a arewa ba sabon abu ba ne mu zaɓi ɗan kudu, mun yi Abiola, mun yi Obasanjo, mun yi Jonathan.

“Kuma ba wanda ya isa ya tilasta mu ya ce dolen-dole ko saboda ban tsoro ko wani abu a ce dole kar wanda ya zabi dan takarar da ba dan kudu ba ko kuma ka da wanda ya jefa ƙuri’a idan ba dan kudu za a jefawa ba.

“Ba wanda ya isa ya yi wannan. Ƴanci muke da shi kamar kowa. Ƴan kudu ɗinnan suna da ƴancin sa ƙuri’a ga wanda suke so. Amma a ce mana mu ba za mu yi ba, wannan kam ba zai yiwuwa ba, in ji kakakin ACF.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *