fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

2023: Fastocin Yahya Bello sun mamaye Yenagoa, Port Harcourt da Warri

Manuniya da allunan talla wadanda ke sanar da kudirin shugaban kasa na Gwamnan Kogi Yahaya Bello sun mamaye jihohin Delta, Ribas da Bayelsa.

Fastocin da allunan talla a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa wanda kungiyar Neja Delta GYB Support Group ce ta dauki nauyinsu.

An kuma kanwata manyan hanyoyi a jihohin uku da Fastocin.

Wani dan gwagwarmayar, Comrade Temple Seriake, ya ce lokaci ya yi da matasa za su karbi ragamar mulkin kasar.

Da yake kira ga Bello da ya fito takarar Shugaban kasa, ya ce: “A matsayinmu na matasa, dole ne mu dauki kaddararmu a hannunmu.

Ya kuma ce ba za suyi shiru ba kuma su yi tsammanin a biya wa matasa bukatunmu, ya zama dole mu tashi tsaya idan muna son cigaban matasa da al’ummar mu.

A karshe yayi kira ga dukkan matasa da su fito kwansu da kwarkwata su yi rijista a APC, domin su mamaye jami’iyyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *