fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

2023: Rashin tsaro ba zai iya hana Kudu maso Gabas samar da shugaban kasa ba – Sanata Ogba

Sanata mai wakiltar Ebonyi ta Tsakiya, Obinna Ogba ya ce kashe-kashen baya-bayan nan da aka yi a Ebonyi da wasu jihohin kudu maso gabas ba zai hana yankin samar da Shugaban kasa na gaba ba.

Mista Ogba ya fadi haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan kudirin da ya gabatar tun farko a zaman majalisar na ranar Laraba.

A cewar Mista Ogba, rikicin ba zai iya hana su samar da shugaban kasa ba, dalili kuwa shi ne, akwai rashin tsaro a wasu sassan kasar amma ba mu dakatar da su ba daga samar da shugaban kasa ba, don haka rashin tsaro ba zai zama hujja ba na hana mu samar da shugaban kasar daga yankin mu ba.

Tun da farko a cikin yunkurin nasa, Mista Ogba ya nuna damuwa game da tabarbarewar yanayin rashin tsaro a kasar wanda a cewarsa, ya yadu a mafi yawan bangarorin kasar.

Ya ce akwai bukatar cikin gaggawa Gwamnatin Tarayya ta magance matsalolin tsaro a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *