fbpx
Sunday, September 26
Shadow

2023: Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya musanta komawa APC

Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya musanta rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yi na cewa ya koma jam’iyyar All Progressives Congress, APC.

Idan za a iya tunawa rahotanni sun yadu a kafafen sada zumunta cewa tsohon shugaban ya nuna sha’awar shiga jam’iyya mai mulki da kuma ficewa daga babbar jam’iyyar adawa, Peoples Democratic Party, PDP.

Rahoton ya lalata jita -jitar cewa tsohon shugaban yana da niyyar sake tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa a 2023.

Mai magana da yawun tsohon shugaban, Ikechukwu Eze, ya bayyana rahoton a matsayin ‘Labarin Karya’, a lokacin da manema labarai suka tuntube shi.

Eze ya bayyana cewa “Rahoton Labarin karya ne kuma idan har ya sauya sheka za’a sanar da jama’a kafufun yada labarai da suka dace.”

Ya kara da cewa maigidan nasa bai koyi tunanin komawa jam’iyya mai mulki ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *