fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

A Abuja ne kawai nake ganin Sojoji da sabuwar Bindigar AK47 amma sauran Najeriya Tsaffi ake basu>>Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume wanda shine shugaban kwamitin dake kula da Sojoji a majalisar tarayya ya bayyana cewa Sojojin dake Abuja ne kawai ake baiwa sabbin Bindigu.

 

Yace amma wanda ke yaki a sauran sassan Najeriya, tsaffi ake basu.

 

Ya bayyana hakane a wani zama da kwamitin nasa yayi da Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad. Ya bayyana cewa ya zanta da sojoji aman lamarin.

 

Ya kuma tambayi cewa me zai sa a rika baiwa Sojoji Biliyan 30 kawai daga kasafin kudin Tiriliyan 13 na Najeriya?

 

Yace sam hakan yayi matukar kadan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *