fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

A biyamu diyyar Miliyan 28 ko mu kashe wanda muke rike dasu>>Boko Haram

Makonnin da suka gabata, Kungiyar Boko Haram ta kai hari kauyen Kwapre dake Jihar Adamawa inda ta sace mutane da dama.

 

A yanzu Kungiyar ta aikawa da Basaraken garin da sakon cewa, ko dai a basu diyyar Miyan 28 ko kuma su kashe mutanen da suka sace din.

 

Arewa Voice ta ruwaito cewa, Mutane 52 ne Boko Haram ta kama a garin kuma ta nemi cewa zata fara karbar haraji daga hannun mutanen garin. Boko Haram ta mamaye garinne saboda yanda yake kusa da dajin Sambisa, sannan basu samun ganin jami’an tsaro sosai a cikinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *