fbpx
Monday, November 29
Shadow

A ci gaba da sulhu da lallabawa amma idan aka saka ‘yan Bindiga cikin ‘yan ta’adda to za’a sakamako mara kyau>>Sheikh Gumi

Babbam malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa, saka ‘yan Bindiga cikin ‘yan ta’adda matsala ce babba.

 

Ya bayyana hakane a wata sanarwa ds ya fitar inda yace duk inda aka ga bafulatani sai ‘yan Bijilante su kasje amma shi idan ya kai hari kauyuka sai a ce ba daudai ba.

 

Yace tabbad ayyukan ‘yan Bindigar ya kama hanyar zama na ta’addanci saboda kashe mutane amma kuma idan aka sakasu cikin ‘yan ta’adda, to lallai kungiyoyin ta’addanci na Duniya zasu samu hadewa dasu.

 

Yace hakan zai sa matasa da basu da aikin yi su shiga wannan aiki da zai kara dagula lamura, malam yace shi a shawararsa shine a ci gaba da sulhu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *