fbpx
Saturday, June 19
Shadow

A karo na biyu, Kasar Amurka ta nemi Najeriya ta janye dakatarwar da ta wa Twitter

Amurka ta sake yin Allah-wadai da matakin gwamnatin Najeriya na toshe dandalin sada zumunta na Twitter a ƙasar, tana mai cewa toshe shafukan zumunta “ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya”.

Cikin wata sanarwa a yau Alhamis, Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken ya yi kira ga Najeriya da ta tabbatar da ‘yancin faɗar ra’ayi.

“Amurka na Allahh-wadai da haramta dandalin Twitter da gwamnatin Najeriya ta yi da kuma barazanar kama masu amfani da shafin,” a cewar wani ɓangare na sanarwar.

“Hana ‘yan Najeriya damar bayar da rahoto da taro da kuma yaɗa bayanai da ra’ayoyi ba shi da muhalli a dimokuraɗiyya. ‘Yancin faɗar ra’ayi a fili ko a dandalin sada zumunta na cikin turakun kafuwar dimokuraɗiyya.

“Muna goyon bayan Najeriya game da yunƙurinta na haɗa kan ƙasa da samar da zaman lafiya. A matsayinmu na ƙawarta, muna kira ga gwamnati da ta mutunta ‘yancin ‘yan ƙasarta ta hanyar janye wannan haramcin.”

Kazalika Amurka ta nuna damuwa game da umarnin da hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta NBC ta bai wa kafofin cewa su goge shafukansu na Twitter.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta kafe cewa Twitter “yana raba kan ‘yan ƙasar” kuma ta sharɗanta wa kamfanin cewa sai ya yi rajista a matsayin kamfanin kasuwanci a Najeriya kafin ta ɗage haramcin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *