fbpx
Monday, November 29
Shadow

A karon farko Abba Gida-Gida yayi magana kan matashin daya yayi tattaki daga Katsina zuwa Kano dan tayashi jaje

Dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2019 karkashi  jam’iyyar PDP, Abba K. Yusuf yayi magana akan matashinnan da yayi tattaki daga Katsina zuwa Kano dan taya shi da Kwankwaso Alhinin rashin nasarar da suka samu a kotun koli.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A wata sanarwa da me magana da yawun Abba K. Yusuf, Ibrahim Adam ya sakawa hannu, ya bayyana cewa, hankalinshi ya kawo kan Matashinnan da yayi tattaki daga Katsina zuwa Kano dan tayasu Alhini kan zaluncin da aka musu a Kotu.

Yace an rika watsawa cewa basu tarbi matashin ba amma abinda ya kamata a sani shine babu wata sanarwa a hukumance da ya samu ko kuma Kwankwaso ya samu na zuwan matashin. Hakanan a lokacin da matashin ya je Kano duka basa Kano suna Abuja amma duk da  haka wasu ‘yan kwankwasiyya Akida sun tarbeshi wanda hakan ke nuna irin karamcin da suke dashi.

Yace sun yaba da karfin gwiwar matashi Kwamared Aminu amma suna jawo hankalin masoyansu dake fadin kasarnan da su gujewa yin irin wannan tafiya me cike da hadari musamman a lokaci irin wannan da ake fama da matsalar tsaro.

Yace su rika musu addu’a daga duk inda suke zata samesu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *