fbpx
Saturday, October 16
Shadow

A KARON FARKO, ZA A SHIRYA FIM TSAKANIN KANNYWOOD, NOLLYWOOD DA HOLLYWOOD

Hukumar Tace finafinai tare da hadin gwiwar  shahararren mai shirya fim na kasar Amurka sun shirya samar da babban fim wanda zai kunshi masu fitowa a fim daga nan Arewacin Nijeriya da kudancin Nijeriya da kuma wasu jarunai daga kasar Amurka.

Malam Isma’el Na’abba Afakallah Babban Direktan hukumar tace finafinai na jihar Kano shine ya sanar da hakan a lokacin da babban mai shirya fim daga kasar Amurka ya kawo ziyara Mr Ugo Mozia.
Samar da wannan fim na daga cikin burin Gwamnatin Kano na kara inganta harkokin samar da fina finan Hausa tare da kokarin daga darajarsu a kasuwannin duniya.
Babban mai shirya film na kasar Amurka Mr Ugo Mozia ya bayyana cewa film din zaa saka masa yarukan Spanish, Chinese tare da French ta yadda zai samu damar zagayawa zuwa dukkan kasuwannin fina finai dake Duniya…
An gudanar da taron tattaunawa akan shirya fim din a babban ofishin hukumar tace finafinai dake Kano, inda manyan masu shirya fim din Hausa suka kasance a wajen tattaunawar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *