fbpx
Friday, May 14
Shadow

A karshe dai Fadar Gwamnatin tarayya ta tonawa Rev Mbaka Asiri

Fadar Gwamnatin tarayya ta fallasa Asirin babban limamin coci, Rev. Fr.  Ejike Mbaka wanda ke neman Shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi murabus ko a tsigeshi saboda matsalar tsaro.

 

A baya dai Jam’iyyar APC tawa Mbaka Barazanar cewa zata tona masa Asiri idan bai maida hankalinsa kan Aikinsa ba ya daina kokarin tada wa mutane hankali a kasa.

 

Kakakin Shugaban kasa, Malam Garba Shehu a wata sanarwa da ya fitar, yace wasu zasu yi mamakin yanda mutumin da ya goyi bayan Shugaba Buhari har sau biyu amma ace yanzu ya juya masa baya.

 

Garba yace Mbaka ya nemi a bashi kwangila ne amma ShugabaBuhari ya ki amincewa. Yace Mbaka ya je fadar Shugaban kasa ganin Shugaba Buhari i da yace da ‘yan Kwangila.

 

Yace Shugaban ya amince masa aka shiga dashi amma kuma da ya nemi kwangilar sai Shugaba Buhari ya ce a kaiwa hukumar data dace kuma ta bi doka wajan tantance neman Kwangilar, Garba Shehu yace kowa yasan Shugaba Buhari wajan rashin karya doka.

 

Yace to wannan dalili ne yasa Mbaka ke jin haushi. Yace basu watsa hotunan ziyarar Mbaka ba saboda yanda watakila idan mabiyansa suka gani ba zasu ji dadi ba.

 

Saidai masu goyon bayan Malamin sun bayyana cewa, shima dan Najeriya ne kuma yana damar da zai nemi kwangilar.

“An outsider distilling the avalanche of verbiage will be surprised that after supporting the President two times to win the Presidency, Father Mbaka has made a complete U-turn, preposterously asking President Buhari to resign or be impeached.

“Here is the point of departure: Father Mbaka asked for a meeting and to the shock of presidential aides, he came accompanied by three contractors. The President graciously allowed them in, and to everyone’s surprise, Father Mbaka asked for contracts as compensation for his support.

“Anyone familiar with President Buhari knows that he doesn’t break the laid-down rules in dealing with contracts or any other government business for that matter. He requested the appropriate authorities to deal with the matter in accordance with the laid-down rules.

“Inside the Villa, discretion prevailed, that if those pictures and requests were made public, the followers would turn against the religious leader. None of it was released. Now, this is what is eating Father Mbaka.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *