fbpx
Saturday, December 4
Shadow

A Arewa kawai muke son a yi amfani da jiragen yakin da muka sayar muki, kada a kashe kowa a Kudu>>Kasar Amurka ta gargadi Najeriya

Kasar Amurka ta gargadi Najeriya kan jiragen yakin super Tucano da ta sayarwa Najeriyar cewa a Arewa kadai take so a yi amfani dasu.

 

Wannan mataki na Amurka ya farune saboda a nata ra’ayin, a Arewa ne kawai ake da ‘yan Boko Haram da aka ayyana a matsayin ‘yan ta’adda.

 

Saidai itama kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra tuni gwamnatin tarayya ta saka ta cikin kungiyoyin ta’addanci kuma ana yawan samun kashe-kashe da kona dukiyar al’umma wanda ake alakanta kungiyar da su a jihohin Inyamurai.

 

Hakan ya fito ne daga bakin wakilin kasar Amurka kan tsaro, Jonathan Finer wanda yawa ‘yan jarida jawabi, yace sun gayawa Najeriya irin yanda suke so ayi amfani da wadannan jirage karara.

 

Da aka tambayeshi ko za’a iya amfani da jiragen kan ‘ya  IPOB? Sai yace jiragen dan magance matsalar tsaro a Arewa ne aka yi cinikinsu, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Finer said, “We are pleased to deepen our security cooperation with the Nigerian government. I think we made it very clear our expectations about this platform where it would be used and in the right way and we are always raising concerns when we have them and that it’s true with all our security partners around the world.

“This is an important platform for security, particularly in the North and we are pleased the transaction is finally concluded.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *