fbpx
Thursday, May 6
Shadow

A yanzu Gwamnatin tarayya ta yadda ta yi amfani da BVN wajan gano masu bukatar tallafi

Gwamnatin tarayya ta amince da amfani da BVN wajan gano masu Bukatar tallafin da take bayarwa ga ‘yan Najeriya.

 

Gwamnatin dai zata fadada yawan mutanen da take baiwa tallafinne kamar yanda ministar tallafawa mutane da da kula da Ibtila’i,  Sadiya Umar Farouk ta bayyana.

 

Ta bayyana hakane a ranar Talata wajan tattaunawa da manema labarai da kwamitin shugaban kasa dake yaki da Cutar Coronavirus/COVID-19 yayi.

 

Sadiya ta bayyana cewa amfani da fasahar zamani wajan gano wanda ke da bukatar tallafin zai fi zama cikin sauki da kuma a bayyane babu wani boye-boye.

 

Tace zasu yi amfani da BVN da kuma lambobin waya wajan gano masu bukatar.

 

Jigo a jam’iyyar APC,Bola Ahmad Tinubu dai ya baiwa gwamnatin shawarar amfani da BVN a baya.

 

Saidai gwamnatin tace zata yi amfanine da masu saka Naira 100 a waya da kuma masu kasa da Naira Dubu 5000 a Asusun Ajiyarsu, abinda ya jawowa gwamnatin caccaka.

 

Amma wannan sabon matakin da gwamnatin ta dauka kamar ta lashe amantane.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

17 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *