fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Abba Kyari ya karyata zargin cin hanci, cewa ya karbi kudi daga Hushpuppi

Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari ya musanta karbar cin hancin daga wani fitaccen dan Instagram din nan, Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce binciken da ake yi ya nuna cewa Hushpuppi ya bayar da cin hanci ga Kyari don kamo wani Kelly Chibuzo Vincent, daya daga cikin wadanda suka hada baki da shi a Najeriya.

Da yake martani kan zargin a safiyar ranar Alhamis, DCP din a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook da aka tabbatar ya ce hannayensa a wanke suke.

A cewar Kyari, babu wanda ya nemi kudi daga hushpuppi, yana mai bayyana cewa hankalin ‘yan sanda shi ne ya ceci rayukan mutane da ake zargin na cikin barazana.

Kyari ya bayyana cewa Hushpuppi ya sanar da ‘yan sanda cewa wani a Najeriya yana barazanar kashe danginsa. Ya kara da cewa shahararren dan mutumin, wanda ya kasance a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, kafin a tsare shi, ya kuma tura lambar wayar wanda ake zargin, inda ya bukaci ‘yan sanda su yi aiki da sauri don ceton danginsa.

Sai dai ya ce an bar wanda ake zargin ya tafi bayan bincike ya nuna sun dade suna abokai da rashin jituwa kan kudi. Kyari ya dage kan cewa bai nemi ko sisin kwabo daga Hushuppi ba, yana mai cewa kawai lokacin da suke tattaunawa game da kudi shi ne lokacin da dan damfarar ya nemi sanin wanda ya ke dinka kayan sawa na kasa da hular sa, ya kara da cewa bayan ya hada dukkan bangarorin biyu, Hushpuppi ya aika da N300,000 a kan biyan dankin kayan biyar.

Kyari ya ce an kai tufafin da hular zuwa ofishinsa bayan haka wani ya tattara su don kaiwa Hushpuppi. Ya bukaci duk mai sha’awar ci gaba da bin lamarin da ya tuntubi Vincent don tabbatarwa.

Ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu, yana mai bayyana cewa za a tozarta wadanda suke kokarin bata sunansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *