fbpx
Friday, May 14
Shadow

Abin baƙin ciki: Yan bindiga sun sake kashe wasu daga cikin daliban jami’ar Greenfield da suka sace

Yan bindigar dake garkuwa da daliban Jami’ar Greenfield sun sake kashe wasu dalibai biyu.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya bayyana hakan a yau 26 ga Afrilu.

Ya kara da cewa an sanar da jami’ar lamarin, sai dai har yanzu bayyana sunayen daliban da aka kashe ba.

Wannan lamarin ya zo ne kwanaki kadan bayan da ‘yan fashin suka kashe uku daga cikin daliban.

Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasir El-Rufai tayi Allah wadai da wannan mummunar aika-aikar da aka yi wa daliban da ba su ji ba ba su gani ba da aka sace yayin da suke ci gaba da neman iliminsu don samun makoma mai kyau.

Gwamnati na mika sakon ta’aziya ga danginsu da shugabannin jami’ar, tare da yin addu’ar Allah ya jikan su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *