fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Abin boye ya fito fili:Ji irin Tawayar da Kungiyar ISWAP ke fama da ita bayan kashe shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Ga dukkan Alamu dai mutuwar Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau na ci gaba da karawa ‘yan Najeriya farin ciki, dan kuwa Raunin Kungiyar dake ikirarin jihadi na kara raguwa.

 

Kungiyar ISWAP da itace ta kaiwa Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau hari wanda har ta kai ga ya kashe kanta, yanzu itama tana fama da kanta.

 

Kungiyar a yanzu bata da tsayayyen Shugaba, ta dakatar da shugabanta, Abu Hafsa inda aka nada Albarnawi a matsayin shugaban riko. Saidai Albarnawi na fuskantar matsin lamba daga sojojin Najeriya da kuma Mabiya Abubakar Shekau da har yanzu suka ki mika masa wuya.

 

Kungiyar na kuma fama da karancin mayaka i da take ta kokarin ganin ta dauki kanana  yara da matasa da basu da yawan shekaru su mata yaki.

 

Hakan ya fito fili ne daga kisan membobin kungiyar 50 da Sojojin Najeriya suka yi a Damboa.

Masanin harkar tsaro, David Otto Endeley wanda shine mawallafin Eonsintelligence ya bayyana haka inda yake inkarin Rahoton BBC dake cewa kungiyar ISWAP na da karfi sosai.

#ISWAP’s power is on the low even after #Shekau’s suicide mission. #ISIS has dissolved its #ShuraCouncil, suspended its #Wali Abu Hafsa making it leaderless. The caretaker leader #Albarnawi is facing opposition from some #JAS members & the #NigerianArmy is not relenting.

 

#ISWAP’s power is on the low even after #Shekau’s suicide mission. #ISIS has dissolved its #ShuraCouncil, suspended its #Wali Abu Hafsa making it leaderless. The caretaker leader #Albarnawi is facing opposition from some #JAS members & the #NigerianArmy is not relenting.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *