fbpx
Friday, January 21
Shadow

Abin da ya sa ban sake aure ba>>IBB

A karon farko, tsohon shugaban Najeriya na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana dalilin da ya sa bai kara aure ba tun bayan rasuwar tsohuwar matarsa Maryam Babangida, wadda ta rasu a ranar 27 ga watan Disamban 2009.

Yayin wata tattaunawa da Trust TV, IBB ya ce zaɓi yin hakan ne domin ya martaba ta.

Kwanan baya dai an yi ta raɗe-raɗin cewa tsohon shugaban na shirin yin wani auren don samun abokiyar zama, amma yayin wannan tattaunawa ya ce ba gaskiya bane.

‘’Ai da ace na yin da kun sani, don haka ban yi ba, ra’ayi na ne kuma wannan’’ in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *