fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Abin takaicine duk da dimbin Arzikin da Allah ya wadata Najeriya dashi amma ana fama da bakin Talauci>>Atiku Abubakar

Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, Abin takaici ne duk da Arzikin da Allah ya wadata Najeriya dashi amma ana samun masu fama da bakin Talauci.

 

Ya bayyana hakane a sakonsa na ranar ‘yanci da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.

 

Atiku ya kara da cewa sam ba abin amincewa bane ace shekaru 61 bayan samun ‘yancin kan Najeriya amma ana fama da matsalar talauci har yanzu.

 

Atiku yace yana jawo hankalin Shuwagabanni a kowane mataki dasu tabbatar da aiwatar da mulkin Dimokradiyya da zai amfani kowa da kowa.

It is regrettable that despite our vast oil resources, extreme poverty and joblessness have remained persistent. There is no excuse that 61 years after independence, extreme poverty is still staring the ordinary citizen in the face.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *