fbpx
Saturday, April 17
Shadow

Abinda mahaifina ya fada min – Yar makarantar Jangebe ta bayyana yadda ta hadu da mahaifinta da yayarta a sansannin masu garkuwa da mutane

Wata yarinya ‘yar shekara 14 da aka sako a makarantar sakandaren mata ta gwamnati, da ke Jangebe, a jihar Zamfara, ta bayyana yadda ta hadu da mahaifinta da kanwarta a sansannin masu garkuwar da mutane.

A wata tattaunawa ta musamman da manema labarai, yarinya mai suna Habiba wanda aka sakaya sunanta sunan mahaifinta, tace mahaifinta yana ganinta ya gane ta.

Yarinyar, wacce ta fito daga karamar hukumar Anka ta Zamfara, ta ba da labarin yadda barayin suka mamaye gidansu watanni uku da suka gabata.

Habiba ta ce mahaifinta ya gargade ta da kar ta bayyana matsayin ta a gun shi, don gudun kada ‘yan bindigar su kashe shi.

Ga yadda tattaunawarta da mahaifinta ta kasance:

Baban Habiba: Habiba, kece?”

Habiba: Na’am baba ni ce

Baban Habiba: Ya mutanen gida, kowa yana lafiya?

Habiba: Eh baba.

Baban Habiba: Kada ki kuskura ki bari su gane cewa ni mahaifin ki ne, domin za su iya kashe ni.

Habiba: Toh baba.

Habiba ta bayyana cewa anyi garkuwa da babanta da yayarta watanni uku da suka gabata bayan wani samame da yan bindinga suka kai gidansu, inda sun ka kashe kawunta.

Ta kuma ce duk kokarin da aka yi don ganin an saki mahaifina da kanwata ya ci tura saboda bukatar makuden kudade a matsayin kudin fansa.

Ta kara da cewa sun yi masa rauni ta hanyar sarar shi da adda da kuma duka.

Habiba tace a lokacin da ta suna dukanshi, sai da tayi kuka, sun ce za su kashe su idan ba a biya fansa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *