fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Abubuwa 10 da ke jawo talauci a arewacin Najeriya

Wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna yadda talauci ya karu a Najeriya, inda ya ce kashi 87 na matalauta a kasar suna zaune ne a arewacin kasar.

Rahoton ya ce talauci a yankin kudu maso kudancin kasar ya yi gagarumar raguwa tsakanin 2011 da 2016.
Kazalika kusan rabin matalautan suna yankin arewa maso yammaci (jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe, Taraba, Bauchi).
To ko wadanne dalilai ne suke janyo karuwar talauci a yankin na Arewa?
Farfesa Garba Ibrahim Sheka da Injiniya Yabagi Sani da Malam Ibrahim Disina sun bayyana dalilai 10 da ke kara yawan talauci a arewacin Najeriya.
1. Imani da kaddara
Masanin tattalin arziki kan harkar makamashi, Injiniya Yabagi Sani, ya ce bambancin tattalin arziki tsakanin arewaci da kudancin Najeriya ya fara ne tun daga yanayin tunaninsu a matsayinsu na al’umma.
“Mutanen arewa suna da yawan alakanta komai da kaddara da kuma Allah maimakon karfin ikonsu.”
“Yan kudu ba su yarda da haka ba. Suna ganin kamar iyawarsu ce take ba su ci gaba. Yana da illarsa amma kuma in ka duba yana da nasa amfanin a fannin tattalin arziki,” in ji shi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

2. Boko Haram
Farfesa Ibrahim Sheka na jami’ar bayero ta Kano ya ce a garuruwan Bama da Gwoza na jihar Borno akwai wata dawa da suke shukawa da rani amma saboda Boko Haram yanzu babu hali.

“A da idan muka wuce abin sha’awa za ka ga dawa koriya shar iya ganinka, amma yanzu babu ko daya, manoman ma su ne a sansanin ‘yan gudun hijirar Boko Haram.

“Mutumnin da zai noma abinci ya sayar amma yanzu sai dai a ba shi abinci a hannu ai kuwa ka ga fatara ta karu,” in ji Farfesan.

3. Bara da roko

Malam Ibrahim Disina yana ganin cewa yin bara da roko suna cikin abubuwan da ke kara wa al’umma talauci.

Malam Disina ya ce Annabi Muhammad SAW ya ce “duk wanda ya bude kofar roko Allah zai bude masa kofar talauci.”

7.Yawan haihuwa

Yawan al’ummar jihohin arewa ya fi na kudu da bambanci mai yawa, kuma hakan a cewar Garba Ibrahim Sheka, “bai amfani arewa ba saboda ba sa samarwa ko kera abubuwa”.

Ya ce: “A arewa ne muke auren mata hudu, mu haifi ‘ya’ya 20 da ‘yan kai. A kudu da wahala ka samu gida mai sama da yara biyar.

“Na san wani mutum, matansa hudu kuma kowacce gidanta daban na haya amma karamin ma’aikacin gwamnatin jiha ne.”

4. Karancin ilimi
Farfesa Sheka ya ci gaba da cewa yanzu samun aikin gwamnati sai da ilimi, ita kuma harkar ilimi an bar arewa a baya, a kudu kuwa kusan gidan kowa akwai shi.

“Za ka ga ko da mutum yana da aikin yi, akan ba shi horo da karin karatu domin a kara yawan abin da yake samarwa da inganta aikin.”

Ya kara da cewa gwamnatoci sun bar ilimin ya tabarbare, sai ayyukan da za a gani kawai suke yi.

Game da wancan mutumin mai mata hudu, Farfesa ya ce: “Ta yaya zai ba ‘ya’yansa ilimi da tarbiyya da sauransu?”

5. Dogaro kan wani mutum
“Wannan abu yana da alaka da yanayin zamantakewar ‘yan arewa domin kuwa a arewa ne za ka ga iyali guda sun dogara kan mutum daya mai arziki,” in ji Injiya Yabagi Sani.

Ya kara da cewa mutane a arewa kan ta’allaka rayuwarsu kan wani da kuma taimakon juna, yayin da a kudu kusan kowa ta kansa yake yi.

Yabagi Sani ya ce duk da cewa taimakon juna abu ne mai kyau amma kuma yana taka rawa a arewa wurin sanyaya gwiwar wasu domin su nemi na kansu.

6. Rashin tallafa wa mata

“Ka san ‘yan arewa ba su fiya son barin mata ba su shiga wasu harkokin na taimaka wa gida ballantana ma su mallaki sana’ar kansu,” a cewar Yabagi Sani.

Ya kara da cewa sai da yanzu ilimi yake kara yawa ake samun matan suna yin karatu, shi ma kuma ba duka ne suke bari matan su yi aikin gwamnati ba.

“Mace ta yi digiri da komai da komai amma sai a ce ta zauna a gida.”

8. Boye kayayyaki lokacin da ake bukatarsu
Sannan akwai wata al’ada a arewacin Najeriya da ma wasu sassa yadda ‘yan kasuwa ke boye haja ko amfanin gona da nufin sayar da su a wani loakci na daban ko da kuwa ana bukatarsu a lokacin.

Malam Ibrahim Disina ya bayyana hakan a matsayin dalilan da ke kawo talauci a kasa.

9. Satar kudin gwamnati
Injiniya Yabagi Sani da Malam Ibrahim Disina sun bayyana satar kudin gwamnati a matsayin hanyar kara yawan talauci a yankin arewa.

Yabagi ya ce “abin takaicin shi ne yadda ‘yan siyasa ke sace kudin al’umma kuma su bai wa iyalansu, maimakon a taimaki al’umma baki daya”.

10. Rashin sanin ya kamata daga matasa da kuma gwamnati
“Yanzu za ka ga ana ta gudanar da shirin horas da matasa kan sana’o’i daban daban kuma a ba su jari, amma sai ka ga sun sayar da kayan sana’ar da aka ba su,” a cewar Farfesa Garba Sheka.

Farfesan ya ce ya taba jagorantar wani shirin gwammnati na horar da matasan, inda aka koya masu sana’o’i ciki har da dinki, amma sai ga shi dan kwangilar da ya sayar wa gwamnati kekunan dinkin yana bin matasan yana saye kekunan daga hannun matasan.

“Sannan kuma kudin da ake bai wa matasan a matsayin jari bai taka kara ya karya ba, wani lokacin kudin ko shago ba za su isa a kama ba.” in ji shi.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *