fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Adadin mutanen da suka mutu a benan Legas yanzu ya kai 36 – NEMAP

Adadin wadanda suka mutu sakamakonr rugujewar ginin bene mai hawa 21 da ke 20, titin Gerrard, a jihar Legas, ya karu zuwa 36.

Mukaddashin kodinetan ofishin hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) reshen jihar Legas, Mista Ibrahim Farinloye ne ya bayyana hakan a wani sako da ya aikewa manema labarai a safiyar ranar Alhamis.

“Ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane 36 – maza 33 da mata uku, yayin da wasu tara suka tsira,” Farinloye ya rubuta.

Wadanda suka tsira sun hada da maza takwas da mace daya.

Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto wadanda suka makale a baraguzan ginin bene mai hawa 21, wanda ya ruguje a ranar Litinin.

Ku tuna cewa an tabbatar da mutuwar mutane 14 a ranar Laraba.

A halin da ake ciki, a ranar Larabar da ta gabata ne gwamnatin jihar Legas ta bayyana sunayen wadanda suka tsira da rayukansu a ruftawar ginin Ikoyi, kuma a halin yanzu suna jinya a asibitin Marina na Legas.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya karanto sunaye da shekarun wadanda suka tsira a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a wurin jiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *