fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Africom: Bukatar Buhari kan rundunar Amurka tamkar dawo da mulkin mallaka ne>>Shehu Sani

Tsohon ɗan majalisar dattawan Najeriya Sanata Shehu Sani ya ce yana adawa da tsarin dawo da hedikwatar rundunar sojoji masu kula da Afirka wato AFRICOM zuwa nahiyar daga mazauninta da ke Jamus.

Sanata ya bayyana hakan ne bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga Amurka ta dawo da rundunar Afirka saboda matsaloli na tsaro.

Gwamnatin ƙasar ta ce kiran wani sauyin matsayi ne ga Najeriya wadda a baya ta riƙa nuna adawa kan yadda ƙasashen yamma ke kafa sansanoninsu a nahiyar Afirka.

Sai dai yanzu matsalolin tsaron da ake fama da su, sun sanya ganin fa’idar kawo rundunar sojojin ta Amurka.

Amma wasu ƴan adawa irinsu Shehu Sani sun ce kiran dawo da hedikwatar rundunar Amurkan ba mafita ba ce, don kuwa matakin zai iya buɗe ƙofa ga wani sabon salon mulkin mallaka da kawo sojojin ƙasashen yamma su zo su karkasa ƙasashe.

Rundunonin ƙetare ba su ne mafita ba’

Sanatan ya ce da zarar an buɗe irin wannan ƙofa to su ma sauran rundunonin ƙasashen masu karfi irinsu Rasha da Burtaniya da Faransa harta Isra’ila da Iran da Saudiya za su shigo.

Yana mai cewa, “kafa irin wannan hedikwatar na buɗe ƙofa ga ƙulla sauye-sauye a gwamnati da tilastawa gwamnatocin Afirka kan wasu ra’ayoyi kuma fitar su akwai wahala”.

“Abin kunya ne a ce har yanzu ƙasashen Afirka na gayyatar turawa duk da shekarun da aka kwashe na daƙile mulkin mallaka.”

Shehu Sanu ya ce muddin irin waɗannan rundunoni suka shigo Najeriya fitarsu za ta yi wahala, domin maganar ta wuce ta tsaro, za ta haifar da gasa ne tsakaninsu.

A cewar Sanata Sani dawowar ƙasashen yamma nahiyar Afirka ba zai kawo karshen matsalolin da ake fuskanta game da tsaro ba, yana mai cewa hadin-kai ake bukata da kafa rundunar tsaro ta Afirka domin yakar matsalolin tsaron nahiyar.

Sai dai Sanatan ya ce akwai bukatar neman taimakon kuɗaɗe da kayan yaƙi wajen cimma waɗannan burukan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *