fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Akalla muggan makamai miliyan 6 ne ke yaduwa a fadin Nageriya>>Abdulsalami Abubakar

Tsohon Shugaban kasa, Abdulsalami Abubakar ya ce akwai sama da muggan makamai miliyan 6 da ke yaduwa a fadin Nijeriya.

Abdulsalami wanda shine shugaban kungiyar zaman lafiya ta kasa (NPC), ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa na kwamitin tare da manyan masu ruwa da tsaki a Abuja ranar Laraba 7 ga Afrilu.

Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya, ciki har da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III; John Cardinal Onaiyekan; Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Kayode Fayemi; Gwamnan jihar Filato kuma shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong; shugabannin addinai, manyan hafsoshin soja, manyan sojoji, ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro.

Ya ce yawaitar makamai ya kara tabarbarewar tsaro a kasar kuma ya yi sanadin mutuwar sama da 80,000.

Ya kara da cewa dole ne yan kasar da jami’an tsaro su hada kai domin ganin an kawar da matsalar tsaron baki daya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *