fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Akwai barazanar shiga sabon yajin aiki a Najeriya yayin da ASUU da Gwamnatin tarayya suka ci gaba da fada kan hanyar biyan Albashi

Gwamnatin tarayya ta karyata cewa ta karya Alkawarin da ta yiwa kungiyar malaman jami’a ta ASUU.

 

Kakakin ma’aikatar Ilimi, Ben Gong ne ya bayyana haka inda yace, inda yace Gwamnatin tarayya ba zata iya yin Amfani da tsarun UTAS da malaman jami’a suka kawo ba wajan biyansu Albashi.

 

Yace tsarin bai bada damar biyan kudin haraji ba wanda kuma malaman ba zata yiyu su rika karbar Albashi ba tare da biyan haraji ba.

 

Saidai a Bangaren ASUU sun bayyana cewa, tsarin IPPIS sam ba zai iya biya musu bukatarsu ba. Dan kuwa a wasu jami’o’in Farfesa na karbar Naira 80,000 sannan manyan Lakcarori na karbar Naira 25,000 a matsayin Albashi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *