fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Akwai fa yiyuwar watakila an kashe mana shugaban mu Nnamdi Kanu>>IPOB ta koka

Haramtacciyar kungiyar IPOB dake son kafa kasar Biafra ta koka da cewa akwai yiyuwar DSS ta kashe mata shugabanta, Nnamdi Kanu.

 

IPOB ta yi wannan koke ne saboda rashin kai Nnamdi Kanu kotu a yau da ya kamata a ace an ci gaba da Shari’ar da ake zarginshi da cin amanar kasa.

 

An dai daga ci gaba da sauraren karar sai watan October.

 

A baya dai an ji cewa Nnamdi Kanu bashi da lafiya inda zuciyarsa ta kumbura, hakanan, wasu Rahotanni sun bayyana cewa, Nnamdi Kanu ya nemi a mayar dashi gidan yari, maimakon ofishin DSS da ake tsare dashi amma aka ki sauraren koken nasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *