fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Akwai yiyuwar korar Abba Kyari daga aiki ko rage masa mukami idan aka sameshi da laifi>>Hukumar ‘Yansanda

Hukumar ‘yansanda ta, PSC ta bayyana cewa za’a yi bincike akan zargin da akewa DCP Abba Kyari kan alaka da dan damfara Hushpuppi.

 

Tace idan aka sameshi da hannu a lamarin akwai yiyuwar a sallameshi daga aiki, ko a rage masa mukami.

 

Abba Kyari ya samu karin girma sosai a aikin dansanda bayan da ka kama manya-manyan masu laifi ciki hadda gawurtaccen dan Damfara me suna Evans.

 

Saidai hukumar tsaro ta kasar Amurka, FBI ta nemi binciken Abba Kyari inda tace yana da alaka da dan Damfara, Hushpuppi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *