fbpx
Monday, November 29
Shadow

Akwai yiyuwar wahalar man fetur saboda barazanar yajin aikin NUPENG

Kungiyar masu ma’aikatan man fetur ta kasa, NUPENG na barazanar tafiya yajin aiki.

 

Idan hakan ta tabbata, ana tsammanin za’a shiga matsalar karancin man.

 

Kungiyar ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin mako 2 ta biya mata bukatarta ko kuma ta tafi yajin aiki.

 

Kungiyar tace ba makawa idan Gwamnati bata saurareta ba, zata tsunduma yajin aiki.

 

Kungiyar ta bayyana rashin biyan albashi da alawus-alawus da sauran wasu bukatu a matsayin abinda ke damunta, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *