fbpx
Friday, April 23
Shadow

Akwai yuwuwar arewa ta fada cikin matsananciyar yunwa>>FAO

Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta yi gargadin cewa yunwa ta tunkaro Arewacin Najeriya da wasu kasashe 20 daban-daban na duniya.

 

Daga cikin kasashen da hukumar ta FAO ta yi gargadin cewa yunwa na tunkarsu sun hada da: Afghanistan, Yemen, Congo, Sudan, Habasha, Haiti da Syria.

 

Hasashen ya ce kasashe 20 da hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta lissafa, ta ce nan da ’yan watanni za su iya fadawa cikin halin matsananciyar yunwa, idan ba a gaggauta yin wani kokarin cetar da yankunan ba.

 

Rahoton wanda na hadin-guiwa ne tsakanin FAO da Cibyar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ya kuma yi nuni da cewa Nan da watan Yuli wadannan kasashe za su shiga matsanancin karancin abinci, don haka akwai bukatar samar da tallafin gaggawa a wuraren da ake ganin matsalar za ta fi shafa matuka.

 

A Arewacin Najeriya kuwa, rahoton ya ce ana tsoron karancin abinci tsakanin watannin Yuni, Yuli da Agusta, sakamakon rikice-rikicen ’yan bindiga da Boko Haram a Arewacin Najeriya.

 

Yaa kara da cewa “Nan da watanni shida akalla mutum miliyan 13 za su iya afkawa cikin gagarumar matsalar karancin abinci da matsananciyar yunwa a Arewacin Najeriya.” rahoton ya tabbatar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *