fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Al’fanun Lemon tsami da yadda ake sarrafashi domin magance Warin kashi, Dattin hakora da sauransu

Ana Amfani da Lemun Tsami wajen kauda Kurajen Fuska, Fimfus,
da Kyasfi, Yana sa fuska ta kara kyau.
Yadda ake amfani da shi, Araba 1-2, rabin za’a goge Fuska dashi, za’ayi Haka na wasu lokuta, Amma a kiyaye Idanu,
kuma kar a shafa a shiga rana se an wanke tukuna.
2-DATTIN HAKORA DA WARIN BAKI,
Ayi amfani da Burushin wanke Baki
da ruwan LEMON TSAMI a wanke Hakora Zasu fita kar, Baki zai bar wari, amma kar arika
wankewa akai-akai sai lokaci-lokaci saboda zai iya raunana karfin hakora.
3-WARIN QASHI (HAMMATA)
idan Ana fama da ciwon warin Qashi,
ko rashin tsaftace Hammata yadda ya
kamata, Idan an shafa LEMUN TSAMI a Hamata zai kauda wannan warin.
4-RAGE KIBA DA TIMBI (TEBA)
wanda ke buqatar haka, ya samu
LEMON TSAMI daya a ruwan sha da bai wuce kofi daya ba, lokaci-lokaci, kiba da tai6a zasu sa6e.
5-RAUNI (CIWO), sabon raunin da bai
wuce Hankali ba, da zarar an matsa mai
LEMON TSAMI zai kame ya warke.
6-RAGE SHA’AWA, ana shan LEMUN
TSAMI da Lipton dan rage sha’awa.
7-MAQYAN-QYARO, ana goge
maqanqaro da LEMON TSAMI akai-akai zai mutu.
8-AMOSANI, ana goga LEMUN TSAMI
a kai bayan an aske gashin kan.
9-QARNI, ana amfani da LEMUN TSAMI wajen kawar da karnin kifi.
AMMA A KULA, idan mace ta yawaita
amfani da Lemon tsami to zai rage mata
sha’awa. Haka mata masu ciki kada su yawaita amfani da Lemon
tsami. Masu Gembon ciki wato Olsa,
su ma su kula wajen shan lemon tsami.
Amma dukkan wadannan zai musu illa ne in sun sha a ciki ba wai shafawa ba.
YADDA AKE AMFANI DA LEMON TSAMI WAJEN GYARAN FATA,
Lemon tsami da zuma; Ki debi rabin cokalin ruwan lemon tsami da kuma
rabin cokalin zuma sai a kwaba su, daga
nan ki shafa a fuskarki na tsawon minti 15, sannan ki wanke da ruwan sanyi. Idan kina da fata mai gautsi to za ki iya
hadawa da man zaitun.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *