fbpx
Friday, January 21
Shadow

Ali Nuhu, Shamsu Dan Iya, Mansurah Isah, Yakubu Muhammad, Baballe Hayatu da sauran manyan jaruman Kannywood sun bayyana goyon bayansu ga Maryam Booth bayan bayyanar Hoton Bidiyonta Tsirara

Bayan bayyanar bidiyon tsiraici na tauraruwar fina-finan Hausa,Maryam Booth a shafukan sada zumunta, Taurarin fina-finan Hausa da suka hada da Ali Nuhu,Mansurah Isa, Sadiq Sani Sadiq,Baballe Hayatu, Falalu A. Dorayi, Yakubu Muhammad, Shamsu dan Iya dadai sauransu sun bayyana goyon bayansu gareta.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ali Nuhu Addu’a ya mata da fatan Alheri inda ya bukaceta data kasance me karfin zuciya kuma Allah ya bata damar cin wannan jarabawa.

Shamsu Dan Iya ya jaddada soyayyar da yakewa Maryam ne inda yace babu abinda zai sa ya daina sonta.

Mansurah Isan ta yabawa Maryam da kuma mata fatan Cewa Allah zai saka mata kan abinda aka mata. Ta kuma yi godiya ga Allah inda tace ta ji dadi da ba aga wani akanta ba. Ta kara da cewa irin wannan abu ba bakon abune ga mata ba, a gidan biki da makaranta kaga na yin wanka tare dadai sauransu, yanzu ne da zamani yazo ake amfani da waya dan tozarci

Hassan Giggs ma ya nuna goyon bayanshi ga Maryam Booth, sauran sune Rahama Sadau, wadda abayan data bayyana cewa Allah ya isar wa Mayam Booth, har wani yake ce mata shin wai me yasa ta saka kanta a wannan harka, bayan a baya wani abu daya hadata da Maryam Booth din har daina bibiyarta ta yi a shafukan sada xumunta? Rahama ta bayar da amsar cewa, a matsayinta na musulma kuma ‘yar uwarta mace dole ne ta tayata Alhini, Uwal Isa West, Teema Makamashi, Maryam Yahaya, Amal Umar dadai Sauransu na daga cikin wanda suka bayyana goyon bayansu ga Maryam.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *