fbpx
Monday, September 27
Shadow

Allah bai yi kuskure ba da yayi mu a matsayin ‘yan Najeriya – Mai Alfarma Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce Allah bai yi kuskure ba da yayi mu a matsayin ‘yan Najeriya.

Da yake magana a taron karrama Jaridar Leadership 2020 da aka yi a Abuja a ranar Alhamis 9 ga Satumba, Sarkin ya ce dole ne ‘yan Najeriya su tashi tsaye don daukar matakin da ya dace domin magance matsalar rashin tsaro ta hanyar bai wa jami’an tsaro hadin kai dari bisa dari.

Ya kuma ce, yan kasar za su shiga mawuyancin hali idan kowane yankin ya ware daban-daban.

Ya kara da cewa dole ne yan Nageriya daga kowane yanki su hada kai idan suna son a samu zaman lafiya da da cigaba a kasar nan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *