fbpx
Monday, November 29
Shadow

Allah Sarki: Hotunan Matashin da barayin waya suka kashe a Kano

Wannan wani matashine da barayin waya suka masa kwace sannan suka kasheshi a Kano.

 

Sunansa Abdullahi Bala dan kimanin shekaru 30, ‘yan uwa da abokan arziki sun rika hawa shafukan sada zumunta suna alhinin rashinsa.

 

An kashe matashin ne ranar Juma’a, 22 ga watan October na shekarar 2021, kamar yanda dan uwansa, Yazid Ali Fagge ya gayawa Daily Trust.

 

Yace ya hau Adaidaita sahu ne zuwa gaisuwa ashe abinda bai sani ba shine duka wanda keciki barayin wayane.

 

Yace sun tambayeshi waya amma yaki basu sai ya jefa waje dan jawo hankalin mutane. Yace anan suka caccaka masa abi a cinya suka tsere.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *