fbpx
Monday, May 10
Shadow

Allah Sarki, ji yanda Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno

Sojojin Najeriya sun dakile harin Boko Haram a Borno.

 

Boko Haram ta kai harinne akan tawagar sojojin 112 Battalion akan motocin yaki. Saidai Sojojin na sane da zuwan Boko Haram din wanda hakan yasa suka taresu.

 

Wata mahiyar Soji ta gayawa Premium times cewa anyi musayar wuta sosai, gumu ya kai gumu wanda har saida ta kai sojojin sun dan ja da baya na wani lokaci kamin daga baya aka kawo musu karin sojoji daga wata runduna dake kusa dasu inda suk sake afkawa Boko Haram din aka ci gaba da musayar wuta.

 

Da Boko Haram suka ga ba zasu yi nasara akan yakin ba, kuma an kashesu da yawa, sai suka tsere, saidai sun tafi da makamai na sojojin da suka kashe ciki akwai wani babban soja da kuma jami’an JTF 6, sannan kuma sun tafi da motocin Hilux 4 na sojojin.

 

Kakakin sojin, Janar Muhammad Yerima ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace sojohi 2 ne kawai aka kashe.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *