fbpx
Sunday, April 18
Shadow

ALLAH SARKI: Matashin Soja Ya Soma Gina Masallaci Kuma Allah Ya Yi Masa Rasuwa

ALLAH SARKI: Matashin Soja Ya Soma Gina Masallaci Kuma Allah Ya Yi Masa Rasuwa

…ana neman taimakon karasa gina masallacin

Wannan masallaci da kuke gani soja ne mai suna Shu’aibu Ibrahim ya fara ginawa kafin komawar sa ga Allah a filin sa dake NARTON Arewa Bulanguwa road gabas da Gidan Bulo, Nguru a jihar Yobe.

Sojan ya rasu ne a jihar Borno yayin artabu da Boko Haram a ranar 18/12/2020. Dan asalin jihar Yobe ne, a karamar hukumar Nguru, yana daya daga cikin sojojin da suka yi shahada a shekarar da ta gabata.

Ginin masallacin ya tsaya a iya linta, kamar yadda kuke gani a hoto, sakamakon abunda ke hannun wakilan dake kula da masallacin ya kare, hakan ya sa aka kira mu domin neman taimakon karasa ginin masallacin.

Ga wanda Allah ya basa ikon taimakawa kama daga siminti, katakon rafta, langa-langa da dai sauran su.

Wanda zai taimakawa ta account zai iya turawa ta lambar bankin wakilin dake kula da aikin masallacin

ACCOUNT NUMBER:- 3087958664
ACCOUNT NAME:- KAWU ABDULLAHI
FIRST BANK

Domin karin bayani ga lambar wakilin; 08064614655

Abubakar Muhammad Shehu 09035805374
Mahammad Brah Garanti 08139627797

Allah yabada ikon taimakawa.

Shi kuma Allah ya karbi shahadarsa, ya sa aljanna ce makomarsa.

Daga π€ππ”ππ€πŠπ€π‘ πŒπ”π‡π€πŒπŒπ€πƒ 𝐒𝐇𝐄𝐇𝐔

Rariya

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


Γ—
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *