fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Allah yasa nayi shahada>>Tsohon Minista, Solomon Dalung

Tsohon ministan wasanni da matasa a Najeriya Barista Solomon Dalung ya ce guguwar Buhari ce ta jefa gwamnatin APC da Najeriya cikin wahalar da ake ciki inda ya ce ta kwashi kunama da maciji da ke harbin mutane.

Solomon Dalung ya ba ƴan Najeriya haƙuri kan halin da ya kira na wahala da ake ciki, yana bayyana fatan Allah Ya sa ya yi shahada da imanin cewa ya kwatanta adalci gwargwado.

Solomon Dalung ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da ya wallafa a ranar Asabar a shafinsa na Facebook da ya nuna shi a zaune mutane sun kewaye shi.

Ya ce: “Abin da nake nema a wurin Allah shi ne ranar da na yi shahada – Allah ya sa na yi shahada da imanin cewa ya yi ni mutum kuma na yi wa kowa adalci gwargwado.”

“Za mu ba ku hakuri, akwai wahala, mu ne APC, mu ne kuka zaɓe mu, mu ne kuka ba mu mulki – idan muka ce yau ba wahala mun zama azzalumai.”

Idan mun ce ma ku komi na tafiya daidai, ba za ku iya ba mu amsa ba – amma idan kun koma gidajenku kun hau darduma sai ku saukar muna da Suratul Munafikun.”

“Saboda haka akwai wahala, wuri ba lafiya – wannan gaskiya ne ana satar mutane ana cinikin mutum kamar buhun masara,” in ji Solomon Dalung.

Tun da farko tsohon ministan ya wallafa wani saƙo a shafinsa na Facebook inda ya ɗora laifin matsalolin gwamnatinsu ta APC ga waɗanda ya ce Buhari ya aminta da su.

Ana ganin Dalung wanda ya lasa a gwamnatin APC a baya, yana waɗannan maganganun ne don yanzu ba a yi da shi a gwamnatin Buhari.

A cikin bidiyon ya ce: “Abin da ya ba mu illa shi ne guguwar Buhari – domin ta kwashi kunawa da maciji da zomo da bushiya duk muna tafiya tare.”

“Idan ka juya za ka ji kunama ta harbe ka idan mun yi gefe bushiya na dukanmu – guguwa ce ta kawo su – ba don guguwa ba da an samu biyan bukata,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa yadda suka ɗauki shugabanci ashe ba haka yake ba – “lokacin da muna kamfen mun ɗauka komi zai tafi daidai amma an yi yamma da kare.”

“Saboda haka haƙuri za a yi – abin da muke nema shi ne mu cika alƙawali kafin wani zabe – idan wani zabe ya zo ba a yi komi ba kowa zai zama kurma.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *